Shirin Obama na rage bashin da ake bin Amirka

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Barack Obama

Shugaba Obama ya bayyana matakan da zai dauka, domin rage dimbin bashin da ake bin kasar Amurka.

A wani jawabi da ya gabatar yau a jami'ar George Washington, Mr. Obama ya ce daukacin Amurkawa sun amfana da kudaden da gwamnati ta kashe a bangaren ilimi da lafiya da kuma tsaro.

Ya ce yanzu yana shirin daukar mafita mai dorewa, ta yadda za a rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da dala triliyan 4 nan da shekaru 12 masu zuwa.

Shirin shugaba Obaman ya ta'allaka sosai akan kara yawan kudaden harajin da masu hannu da shuni ke biya, da kuma rage kudaden da gwamnati ke kashewa.