An hana yiwa Mamadou Tanja daurin talala

Malam Mamadou Tanja
Image caption Malam Mamadou Tanja

Hukumomin Nijar sun dauki matakin cigaba da tsare tsohon shugaban kasar, Malam Mamadou Tanja, bayan da a yau kotun daukaka kara ta yanke hukuncin yi masa daurin talala.

Kotun daukaka karar ta yankewa tsohon shugaban hukuncin daurin talalar ne, akan tuhumar da majalisar mulkin sojan kasar ta CSRD ke yi masa, ta yin almundahana da kudaden kasar kimanin Biliyan 3 na CFA - kwatankwacin Euro miliyan 2 - a lokacin da yake mulki .

Jim kadan bayan haka ne hukumomin kasar suka sake daukar wani matakin ci gaba da tsare Malam Mamadou Tanjan, a gidan kurkukun garin Kollo, inda dama ake tsare da shi.

A hira da BBC, lauyan tsohon shugaban, Maitre Souley Oumarou, ya ce matakin yana da nasaba da siyasa.