Isra'ila ta hallaka Falasdinawa akalla uku

Harin da Isra'ila ta kai a yankin Gaza Hakkin mallakar hoto L
Image caption Harin da Isra'ila ta kai a yankin Gaza

Wani hari wanda dakarun sojan saman Isra'ila suka kaiwa kudancin yankin Gaza ya kai ga hallaka akalla Falasdinawa uku.

Dakarun Isra'ila dai sun ce manufar kai harin ita ce samun wata mota wadda suka yi zargin tana dauke da wadansu mayakan kungiyar Hamas wadanda ke shirin sace wasu 'yan kasar ta Isra'ila a daidai lokacin wani hutun bukukuwan addini na Yahudawa.

Hamas dai ta tabbatar da cewa ta yi asarar mambobinta da dama sakamakon wannan hari.

A watan da ya gabata dai tashe-tashen hankula tsakanin Isra’ila da Falasdinawa sun karu matuka.