'Ba da manufa Isra'ila ta cutar da mutane ba'

Richard Goldstone
Image caption Richard Goldstone

Isra'ila ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da wani rahoto wanda ya ce ta aikata laifuffukan yaki lokacin da ta kai hari zirin Gaza tsakanin watan Disamban 2008 da watan Janairun 2009.

Kiran dai ya biyo bayan wallafa wata kasida wadda marubucin rahoton, Richard Goldstone, ya yi a jaridar WashingtonPost, yana cewa yana tunanin sake shawara.

Mista Goldstone, wanda masanin shari'a ne dan kasar Afirka ta Kudu, ya rubuta cewa da ya san abin da ya sani yanzu, da rahoton nasa ya sha bamban.

A cewarsa, wani bincike da rundunar sojin Isra'ila ta wallafa, kuma wani kwamitin Majalisar Dinkin Duniya ya sa masa albarka, ya nuna cewa Isra'ila ba ta kai hari kan fararen hula da manufa ba.

Ya kuma ce ya yi takaicin yadda kasar ta Isra'ila ta ki ba tawagarsa hadin kai lokacin da suka je bincike a kan al’amarin.

Yanzu dai Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da rahoton.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Netanyahu ya ce ba da gangan Isra'ila ta cutar da fararen hula ba.

Mista Goldstone ya ce Isra'ila ta gudanar da bincike mai zurfi a kan zarge-zargen aikata ba daidai ba, amma kungiyar Hamas mai mulki a zirin na Gaza ba ta gudanar da bincike ba.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta Hamas ba ta mayar da martani ba.

Karin bayani