Yanayin rayuwa a Abidjan ya tabarbare

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

Yanayin rayuwa a birnin Abidjan na kara tabarbarewa yayin da ake ci gaba da fuskantar kiki kaka a yunkurin da sojoji masu biyayya ga Alassane Ouattara ke yi na tumbuke Laurent Gbagbo daga karagar mulkin Ivory Coast.

A halin da ake ciki dai mazauna birnin na Abidjan ba sa samun ruwan sha ko wutar lantarki; akasarin asibitoci da shaguna kuma a rufe suke yayin da abincin da ke hannun jama'a ke daf da karewa.

A wani jawabin da ya yi ta gidan talabijin a daren jiya Alhamis, Mista Ouattara, wanda duniya ta amince da shi a matsayin zababben shugaban kasar, ya zargi Mista Gbagbo da jefa al'ummar birnin cikin kunci da rudani.

“Abin bakin ciki, taurin kan shugaban kasa mai barin gado ya jefa al'ummar Abidjan cikin tsananin bala'i ta fuskar tsaro da kuma zamantakewa”, inji Mista Ouattara.

Ya kuma kara da cewa, “Mako guda ke nan mazauna Abidjan na garkame a cikin gidajensu saboda tsananin tsoro; ga wahalhalun rayuwa—kama daga rashin ruwa da rashin wutar lantarki zuwa karancin abinci da magani—sai karuwa suke yi a kullum”.

Mista Ouattara ya kuma ce ya nemi Babban Bankin Kasashen Afirka ta Yamma ya bude rassansa a kasar ta Ivory Coast don a samu damar biyan ma'aikata albashinsu.

Ya kara da cewa Mista Gbagbo ya kewaye kansa a fadar shugaban kasa da manyan makamai da kuma sojojin haya, to amma an yi masu kawanya don tabbatar da tsaron lafiyar mutanen da ke yankin.

Magoya bayan Mista Ouattara dai sun ce manufar su ita ce kama Mista Gbagbo da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Sai dai kuma kungiyaoyin agaji a kasar ta Ivory Coast sun ce aikin agaji ba ya tafiya yadda ya kamata saboda matsalar tsaro.

Wani ma'aikacin kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ya shaida wa BBC cewa a ko wanne lokaci mazauna birnin na kiran jami'an kungiyar ta waya don neman taimako amma ba damar taimaka masu.

Wata mata a birnin ta bayyana cewa ba a samun ruwan sha a unguwar da take kuma nan da kwanaki biyu ruwan da ta tanada zai kare.

Ta kuma ce ko da yake a inda ta ke babu tashe-tashen hankula, danginta da ke wani sashe na birnin suna cikin halin ha'ula'i:

“Ba su da abinci kuma ba mu san yadda za mu yi mu kai musu ba.

“Suna cikin matukar wahala saboda kwanakinsu uku ke nan ba su samu abin da za su ci ba”.