Ana ci gaba da gwabza fada a Ivory Coast

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fada ya yi kamari a 'yan kwanakin nan

Dakarun da ke biyayya ga mutumin da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin zababben shugaban kasar Ivory Coast Alassane Outtara, na gwabza kazamin fada daura da gidan abokin hamayyarsa Laurent Gabgbo.

Dakarun da ke biyayya ga Alassane Outtaran dai, sun yi ta kai hare-hare a kan yankuna da dama na babban birnin kasar Abidjan, wadanda har yanzu suke karkashin ikon Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga mulki.

Wani mazaunin birnin na Abidjan ya shaida wa BBC abin da ke faruwa a garin:

"Yace ana jin karar harbe-harbe masu karfi a koina, kamar abubuwa suna fashewa. Fashe-fashen sun fi na jiya yawa, al'amarin abin trsoro ne.

Magoya bayan Mr. Gbagbo sun ce har yanzu yana cikin birnin.