Bom ya tashi a kusa da Kadunan Najeriya

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Wadansu abubuwa wadanda ake zaton bama-bamai ne sun fashe cikin daren jiya Alhamis a Mahuta, wani yankin da ke bayan garin Kaduna, a arewacin Najeriya.

Wakilin BBC wanda ya je wurin da al’amarin ya faru ya ce abin—wanda ake zaton bam ne—ya tashi da wadansu mutane su biyu wadanda aka samu a cikin mawuyacin hali, kuma tuni daya daga cikinsu ma ya riga mu gidan gaskiya.

Ga alamu dai mutanen ne suka hada wadannan bama-bamai guda hudu a wani kango a bayan garin na Kaduna, ana kuma zaton sun dauki daya daga cikin bama-baman ne za su dana.

Jami’an tsaro dai sun tabbatar da faruwar wannan al’amari sun kuma ce sun kama wadansu mutane da ake zargin abokan masu mu’amala da bama-baman ne.

Jami’an sun kara da cewa suna ci gaba da bincike a kan al’amarin.