Yau ake fara zaben majalisa a Najeriya

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

A Najeriya, yau ne ake gudanar da zaben da ake saran masu zabe sama da miliyan saba'in da uku za su fito don kada kuri'unsu.

Yau din dai 'yan Najeriya za su zabi 'yan Majalisar Dokoki ne na kasa.

Zaben na yau dai yana da matukar muhimmanci saboda shi ne zai share fagen sauran zabubbukan da za a yi, cikinsu har da na shugaban kasa, kuma watakila ya kasance manuniya dangane da makomar zabubbukan.

Najeriya dai na fuskantar kalubalen shirya sahihin zabe, saboda masu sa-ido a kan zabe na gida da na kasa-da-kasa sun yi zargin cewa zabubbukan da kasar ta gudanar a shekarun 2003 da 2007 duka suna cike da magudi sakamakon matsalolin da suka shafi satar akwatunan zabe da musgunawa masu kada kuri'a

Yayin wannan zabe dai 'yan takara za su fafata ne domin lashe kujeru dari da tara a Majalisar Dattawa, da kuma wadansu kujerun dari uku da sittin a Majalisar Wakilai.

Yanzu dai idon duniya na kan Najeriya, musamman ma saboda gwamnatin kasar ta sha alwashin gudanar da sahihin zabe a wannan karon.

Karin bayani