Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Talauci da magudin zabe

Duk lokacin da aka yi batun magudin zabe a Nigeria, babu wandanda ake hange a matsayin su kadai ke da hannu kamar yan siyasa da jami'an tsaro da kuma jami'an hukumar zabe.

Sai dai matasa sune ake ga yan siyasar na amfani dasu wajen kwace akwatuna da ma sauran hanyoyi na magudi, inda su kuma suke basu na goro.

Matasa da dama dai su kan bari ayi amfani dasu wajen magudin zabe, inda suke fakewa cewa talaucine ya tilasta musu yin hakan.

Wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya hada mana rahoto kan yadda yan siyasar kan yi amfani da matasa wajen magudin zabe a Nigeria.