Ban Ki-Moon ya yi tir da harin Afghanistan

Ban Ki-Moon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya bayyana harin da aka kai kan ma'aikatan Majalisar a Afghanistan da cewa abu ne mai tayar da hankali.

Akalla mutane goma sha hudu ne dai suka rasa rayukansu, ciki har da ma'akatan Majalisar su bakwai bayan wasu masu zanga-zanga sun cinnawa ginin majalisar Dinkin Duniyar wuta a garin Mazar-i-Sharif.

A cewar Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya, babu wani abin da za a iya fada don ya zama uzuri dangane da farwa ma'akatan Majalisar.

Jami'an tsaro a kasar ta Afghanistan sun ce a cikin wadanda suka rasa rayukan nasu har da wadansu masu gadi, wadanda aka kwashe makamansu.

Jamiā€™an tsaron sun kuma ce wadansu daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu harbe su aka yi, yayinda aka fillewa mutane biyu daga ciki kai.

Malaman kasar ta Afghanistan ne dai suka yi kira a yi zanga-zanga a lokacin sallar Juma'a don nuna rashin amincewa da kona Al-Kur'anin da aka yi a Amurka kwanaki goma sha uku da suka wuce.

Daya daga cikin masu zanga-zangar dai ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar cewa za su kaddamar da Jihadi a kan Amurka idan ba ta hukunta wadanda suka kona Al-Kur'anin ba.