Rawar da Mata suke takawa a harkar siyasa

Mata a ko wace kasa kan taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban dimokaradiyya ta hanyar bayar da gudumawa wajen kada kuri'a har ma wajen fitowa yakin neman zabe domin tabbatar da cewar jam'iyar da suke marawa baya ta kai ga nasara.

Sai dai a kasashe masu tasowa kamar Najeriya har yanzu matan sune koma baya wajen cin gajiyar demokaradiyyar sakamakon irin koma rashin samun cikakken samun damar fitowa takara ko kuma rike mukaman siyasa yadda ya kamata ta yadda sauran matan musammam mazauna karkara zasu samu wakilci a Ma'aikatun gwamnati ko kuma Majalisun Jihohi da na Tarayya.

A yayin da dai matan ke ganin mazan ne keyi musu kakagida wajen samun irin wannan dama wasu kuwa cewa suke su kansu matan basa marawa yan uwansu matan baya wajen tsayawa takarar, lamarin dake haifar da irin koma bayan da suke fusknata a siyasar kasar.

Wakiliyarmu dake Maiduguri Bilkisu Babangida ta hada mana rahoto na musamman game da wannan batu.