Martani kan dage zaben Najeriya

Martani kan dage zaben Najeriya
Image caption A wasu wuraren dai har an fara kada kuri'a kafin a dage zaben

'Yan siyasa da kungiyoyin fararen hula na ci gaba da maida martani a kan sanarwar da hukumar zaben Najeriya ta bayar na dage zaben 'yan Majalisa da aka shirya yi a ranar Asabar.

Shugaban Najeriyar Dr. Goodluck Jonathan ya ce ai anyi sa'a da ba zaben shugaban kasa ne aka daga ba.

Dage zaben da ya zo kwatsam, kuma ya batawa masu kada kuri'a da dama rai.

Shugaba Goodluck ya ce "Idan da za a yi zabe cikin kwana biyu ko daya mai inganci, babu laifi ayi hakan, don daga bisani ayi zabe mai gaskiya".

Sai dai a wata sanarwa da ta aikewa BBC, gamayyar kungiyoyin fararen hula ta Project 2011 Swift da ta TMG, cewa suka yi sun yi mamakin dage zaben.

A cewarta, kamata ya yi INEC ta dage zaben tun a daren ranar Juma'a.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Civil Rights Congress of Nigeria, cewa ta yi koda yake ya zama wajibi a dage zaben, amma za a iya kaucewa faruwar hakan.

Don haka ta yi kira ga a gaggauta bincike kan abubuwan da suka kai ga dage zaben.