INEC ta dage zaben 'yan majalisu

Image caption An samu jinkirin kawo kayan zabe

A Najeriya hukumar zaben kasar ta sanar da dage zaben `yan majalisar dokokin kasar zuwa ranar Litinin mai zuwa.

Hukumar ta ce rashin isar kayan zabe zuwa bangarorin kasar da dama na daga cikin dalilan da suka janyo dage zaben.

Wannan lamari dai ya katse hanzarin miliyoyin `yan kasar da suka fita kwansu-da-kwarkata don su kada kuri`unsu.

Tun da jijjifin safiyar yau din nan `yan Najeriya da dama, wadanda suka cancanci kada kuri`a suka yi tururuwa zuwa rumfunan zabe domin kada kuri`unsu.

Sai dai tun a farkon fara ayyukan zaben wasu alamun tangarda suka fara bayyana a birnin tarayya Abuja da jihar Ribas da Plateau da kuma Borno.

Jinkirin kawo kayan zabe

Rahotanni daga sassan kasar da dama sun ce an samu jinkiri wajen fara tantance ma su zabe, amma wannan matsala ba ta sanyaya gwiwar masu kada kuria`a ba.

Haka dai masu kada kuri`ar suka yi ta jiran gawon shanu, har sai bayan rana ta take bayanai masu katse hanzari suka fara fitowa daga mahukuntan Najeriya cewa an dage zaben sai ranar Litinin mai zuwa saboda wasu dalilai.

"A yanzu haka dai ina da takadar kada kuri'a a zaben 'yan majalisar wakilia, amma bani da takardar sakamakon zabe. A na Majalisar dattawa kuwa ba ni da takardar kada kuri'a da kuma na sakamako." In ji Maria Owi, Kwamishinan hukumar zabe na Jihar Akwa Ibom a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Jega dai ya alakanta jinkirin da aka samu ga jinkirin shigo da kayan zaben daga wajen kasar, amma ya nuna kwarin gwiwar gudanar da zaben a ranar Litinin mai zuwa.

Wannan batun fasa zaben dai watakila zai iya shafar martabar Hukumar zaben Najeriyar da gwamnatin kasar a idon masu sa-ido a kan harkokin zabe cikin gida da na kasa-da-kasa da kuma kasashen duniya dangane da ikirarin da suke yi na gudanar da sahihin zabe a kasar.

Yayin da a daya hannun kuma zai janyo yanke-kauna da cire tsammani a zukatan `yan Najeriyar da dama dangane da fatansu na samun sahihin zabe.

Duk da cewa hukumar zaben Najeriya ta gabatar da hanzarinta na dage zaben, maimakon uzurin nata ya gamsar da `yan kasar, watakila zai janyo wasu tone-tane game da gaskiyar abin da ya haddasa dage zaben, musamman ma da yake hukumar zaben ba ta nuna ta na fuskantar wannan matsalar ba har zuwa jajibirin zaben.