Babu bayani kan kisan kiyashin da aka yi a Duekoue

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Kot Divuwa suna can suna kokarin kare dubban fararen hula da suka sami mafaka a wata coci da ke garin Duekoue a yammacin kasar, inda aka ba da rahoton kisan mutane dari takwas a fada a makon jiya.

Wkilin BBC a garin na Duekoue ya ce halin da ake ciki na dardar ne da rashin tabbas.

Ya ce an kwashi ganima sosai tare da yin barna, ya kuma ga akalla gawawwaki ashirin a bakin titi, ana kuma kara ganin wasu a cikin itace da ciyawa.

Jami'an dakarun da ke biyayya ga Alassane Ouattara sun ce kamar mutane dari da sittin ne aka kashe a garin, a fafatawa tsakarin dakarun da ke fada.

Sun bayyana batun kisan gillar da aka ce an yi da cewa ba gaskiya ba ne.

Fada ya sake barkewa nan da can a birnin Abidjan na Kot Divuwar.

Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Abidjan, Hamadou Toure, ya ce ana ta musayar wuta a kewayen fadar shugaban kasa.

Dakarun da ke biyayya ga Alasanne Ouattara sun kafa dokar hana yawo a birnin.

Game kuma da inda Laurent Gbagbo shawara daga nan Turai, Toussaint Alain, Mr Gbagbo yana nan cikin kasar.

Ya ce, "Na ce Shugaba Gbagbo yana nan a fadar shugaban kasa, inda ya saba aiki, yana kuma fuskantar matsalar tare da wasu rukunin mutane da aka kebe don fuskantar matsalar da ke tasowa daga daga wajen kasar."

Wani mazaunin birnin ya shaidawa BBC cewa gungun mutane dauke da makamai na karakaina a kan tituna.

“Ina iya ganin wadansu mutane farar hula su hudu ta taga, wadanda suka rufe fuskokinsu, dauke da bindigogin Kalashnikov”, in ji mutumin, wanda ba ya so a ambaci sunansa.

Ya kara da cewa, “Ga wadansu can kuma [ina hango su] su takwas sanye da wando jeans suna gangarowa—akasarinsu suna rike da bindigogi”.

Dakarun Mista Ouattara sun ce suna fadan karshe ne, amma ga alamu suna fuskantar matsananciyar turjiya.

Karin bayani