'yan tawayen Libya sun amsa rashin da'ar mayakansu

Jirgin saman yaki na kungiyar NATO Hakkin mallakar hoto RTV
Image caption Jirgin saman yaki na kungiyar NATO

Dakarun da ke adawa da shugaba Gaddafi, wadanda ke cigaba da fafatawa don neman iko a kan garin Brega mai arzikin mai a gabacin kasar, shugabanninsu sun amsa cewa rashin da'ar dakarunsu ne suka jawo masu kai hari daga jiragen saman kungiyar tsaro ta NATO ranar Juma'a.

'Yan tawayen Libyar sun amsa laifinsu game da harin da dakarun kungiyar NATO suka kai masu, kamar yadda jagoran gwamnatinsu ta wucin gadi, Mustafa Abduljalil ke cewa.

Ya ce, "Abinda muke cewa shi ne, laifin na dakarun sa-kai ne, wanda suka yunkura zuwa gaba, suka yankin da jiragen sama ke kai hari, wannan kuma ba laifi ne da za a dora ma NATO ba.