Jama'iyun hamayya a Najeriya sun nemi dage zaben gobe

Gamayyar jam'iyyun hamayya a Najeriya sun yi kira ga hukumar zaben kasar, wato INEC, suna cewa ta sake dage zaben majisun dokokin tarayar kasar, wanda za'a gudanar a gobe, Litinin.

A cewar jamiyyun, hukumar zaben tana bukatar karin lokaci domin shawo kan kuran-kuran da aka fuskanta, yayin da aka yi kokarin gudanar da zaben a jiya Asabar - kura-kura tilasta daga zaben zuwa gobe.

Sai dai hukumar zaben ta ba da tabbacin cewa komai zai tafi lami lafiya a zaben a gobe.