Amurka ta bukaci 'yan kasarta su bar Syria

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Amurka ta shawarci 'yan kasarta dake Syria dasu tattara ina -su -ina -su su bar kasar saboda gudun barkewar wani sabon rikici

Kasar Amurka ta shawarci 'yan kasarta dake kasar Syria da su fara duba yiwuwar barin kasar, saboda yiwuwar barkewar tashin hankali sakamakon zanga zangar 'yan adawa da kuma gwamnatin Syrian.

Mahukunta a Amurka sun bada tayin kwashe ma'aikatan gwamnatin Amurkar da iyalansu a can, kyauta.

An dai halaka mutane da dama sakamakon zanga zangar da aka yi a kasar cikin makonnin baya bayan nuna adawa da shekaru 11 da mulkin shugaban kasar Bashar al-Assad, wanda 'yan gidansu suka dauki shekaru arba'in suna yi.