An kaddamar da sabbin harehare a Abidjan

Ci gaba da gumurzu a birnin Abidjan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Mr Ouattara sun ce sun kaddamar da harin karshe

Majalisar dinkin duniya ta ce dakarunta a kasar Ivory Coast sun yi barin wuta da jiragen helikopta a fadar shugaban kasa da ke Abidjan, wato mazaunin Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga mulki bayan faduwa zabe a bara.

Wakilin majalisar dinkin duniya a Ivory Coast, Choi Young-jin ya zargi magoya bayan Mr. Gbagbo da kai hari kan dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar.

Harin ya zo ne bayan da Faransa ta baiwa jami'anta da ke Abidjan izinin shiga ayyukan majalisar dinkin duniya.

A halin yanzu, dkarun Mr Ouattara sun ce sun kaddamar da harin a yi-ta-ta-kare a birnin na Abidjan.