An yi tankiya tsakanin Jega da Gwamnati

Rahotanni daga Najeriya sun yi zargin cewa an samu takun-saka tsakanin fadar shugaban kasa da kuma hukumar zabe mai zaman-kanta ta kasar, sakamakon tangardar da aka fuskanta, da ta kai ga dage zabe zuwa ranar Asabar mai zuwa.

Wasu rahotannin sun dora wa bangaren shugaban kasa alhakin matsalar rashin kai kayan aikin da aka samu, yayin da wasu ke cewa matsala ce ta cikin gidan hukumar zaben.

A cewar rahotannin, rashin gudanar da zaben ya sa majalisar tsaron kasa yin wani zama da shugaban hukumar zaben, inda suka yi wata zazzafar tattaunawar da ta kai ga shugaban hukumar yin barazanar murabus daga aiki, bayan an nemi yayi wasu sauye sauye.