Shugaba Obama zai nemi wa'adi na biyu a 2012

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto Other
Image caption A shekara ta 2008 ne aka zabi shugaba Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara karo na biyu a zaben da za a gudanar a shekara ta 2012.

Mr Obama ya wallafa wani hoton bidiyo a shafinsa na intanet sannan ya aika sakon e-mail ga magoya bayansa yana bayyana musu aniyarsa ta tsayawa takarar.

Shugaban na da miliyoyin magoya baya a yanar gizo, kuma ana yiwa shafin yakin neman zabensa kallon babban hanyar da ta taimaka masa wurin yin nasara a zaben shekara ta 2008.

Sanarwar dai ba ta zo da bazataba, kuma ana saran masu yakin neman zabensa za su fara raba takardun zabe a wannan makon.

Sama da shekaru 40 kenan, rabon da wani shugaban Amurka ya ki neman tazarce.

A daidai lokacin da ake tsakiyar yakin Vietnam a 1968, Lyndon Johnson ya mamayi jama'ar kasar, bayan da ya bayyana cewa ba zai nemi tazarce ba.