Kalubalen dake tattare da yakin neman zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ACN

A Najeriya sake daga soma manya zabukan da hukumar zaben kasar tayi zuwa karshen mako ya sake bude wa 'yan siyasar kasar kafar ci gaba da yakin neman kuri'u.

Sai dai a jahohi da dama ana zargin cewar matsanancin amfani da kudi ne akeyi wajen neman kuri'un a maimakon gangamin yekuwar neman zabe da doka ta amince da shi.

Sake daga zabubukan shiga majalisun kasar da hukumar zaben kasar tayi ya bankado zarge-zargen amfani da kudaden gwamnati wajen sayen kuriu da kuma toshe bakin malaman zabe daga yan siyasar da ke kan mulki a yawancin jahohin kasar.

Wannan lamari na faruwa a musamman wuraren da 'yan kuri'unda aka fara jefawa suka nuna alamun reshe zai juye da mujiya.

Jihar kebbi wadda ke shiyar Arewa maso Yammacin kasar wadda kuma ita ce mahaifar shugaban hukumar zaben kasar da kuma mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP mai mulki na daga cikin inda 'yan hamayya ke zargin jami'an gwamnati da na jam'iyya mai mulki da cimma matsayar fitarda sama da Naira Biliyan biyu domin sayen kuri'u gabanin zaben da yan majalisun kasar mai zuwa.

Alhaji Abubakar Malam dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar hamayya ta CPC na daga masu wannan zargin.

Sai dai gwamnatin jahar ta Kebbi tabakin mai baiwa gwamnan jahar shawara kan bin ka'idoji wajen fitarda kudaden gwamnati Barista Aminu Usman, ta musanta cewar za'a yi anfani da kudin ne wajen sayen kuri'u.

Batun anfani da kudi wajen sayen kuri'u ba bakon abu bane a kasar, kuma duk da kasancewar ba abune da dokar kasar ta halatta ba.

Amma kusan za'a iya cewa ya zama wani sharadi ga cin zabe ko samun kuri'u masu yawa saboda yadda masu zabe da dama a kasar ke amincewa da sayarda kuri'unsu ga 'yan siyasar da a hakikani ba sune zabinsu ba.

Yayin da aka koma yakin neman zabe gadan-gadan a Najeriya, 'yan adawa a kasar na kokawa da yadda suka ce jami'an tsaro na muzguna masu ta hanyar amfani da umarnin gwamnati, zargin da su kuma jami'an tsaron ke musantawa.

Takun saka tsakanin abokan hamayya

Tunkarar muhimman zabuka ne a tsarin dimokuradiyyar mai tattare da kalubale, na tashe-tashen hankula da kuma zazzafan takun saka tsakanin bangarori masu hamayya da juna.

A jihar Gombe alal misali, hukumomin tsaro sun kama mutane sama da arba'in, wadanda 'yan adawa suka ce mutanensu ne bayan wata hatsaniya ta siyasa a yankin Pindiga lamarin da ya kara fito dakalubalen siyasar Najeriyar a fili.

A baya-bayan nan dai jami'an tsaron sun kama mutane sama da arba'in a karamar hukumar Pindiga, bayan wani tashin hankali da aka yi tsakanin 'yan jam'iyar PDP mai mulki da kuma 'yan jam'iyyar adawa ta ANPP, inda mutum guda ya rasa ransa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Magoya bayan jam'iyyar PDP a taron Siyasa

Malam Aliyu Abdu daya ne daga cikin jami'an yakin neman zaben dantakarar gwamna na jam'iyyar ta ANPP a jihar Gombe, kuma ya ce bayan faruwar lamarin jami'an tsaro sun kama wasu jiga-jigan 'yan-jam'iyyar a yankin na Pindiga.

Kakakin run dunar 'yansandan jihar ta Gombe, ASP Ahmad Doma, ya tabbatar mani da kama mutane arba'in da biyar a lamarin na Pindiga kuma ya ce har sun gurfanar da su a kotu.

Wakilin BBC ya ci gaba da yi masa tambayoyi kan rade-radin cewa sun yi yunkurin kama wani babban jami'in yakin neman zaben shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Alhaji Abu Mu'azu.

Alhaji Abu Mu'azu dan jihar Gomben ne wanda kuma rahotanni ke cewa basa jituwa da gwamnan jihar.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan ya ce sai dai in tuntubi mai gidansu, wato kwamishinan 'yansandan jihar wanda shi kuma ya ce lallai an sami hatsaniya amma ya musanta cewa sun yi yunkurin kama wani dan siyasa a filin jirgin saman, kuma ya ce basa karbar umarni daga gwamnan jihar ta Gombe, Muhammad Danjuma Goje.

Takun tsaka tsakanin 'yan adawa da gwamnatin jihar Gomben dai ya yi kamari ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Danjuma Goje na fuskantar barazana a zaben dake tafe a kokarinsa na shiga Majalisar Dattijan Najeriya, ko da yake dai su 'yan bangaren gwamnan cewa suke yi babu wata barazana.