Takaddama tsakanin gwamnatin da 'yan adawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Taron siyasa

Yanzu haka wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da kuma jam'iyyun adawa a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta gano wani shiri da 'yan adawar ke yi na haddasa tashe-tashen hankula a jihar da nufin kawo cikas ga zabukan dake tafe.

To sai dai kuma jam'iyyun adawar sun musanta zargin, kana suka maida wa gwamnatin martini da cewa ta tsorata ne da zabukan na tafe kuma hasali ma ita ke haddasa tashe-tashen hankula a jihar, ta hanyar amfani da 'yan sara-suka.

Wannan lamari dai na faruwa ne yayin da ya rage kwanaki kadan a gudanar da zabukan da hukumar zabe ta kasar wato INEC, ta sake tsara jadawalinsu a duk fadin Nijeriya.

Rikicin kabilanci da addini

Gwamnatin jihar Bauchin dai ta zargi 'yanadawar da shirin tayar da hanakali a yankunanan Tafawa Balewa da Bogoro inda ake yawaman samun rikice-rikice na kabilanci da kuma cikin garin Bauchi, ta hanyar amfani da 'yansara suka da tace sun yi hayarsu.

Malam Sanusi Muhammad shi ne mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara kamn harkokin watsa labarai.

"Gwamnati na yin dukumai yiwu domin mu tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, amma muna da labarin cewa 'yan adawa na kokarin tayar da rikici a lokacin zabe". In ji Malam Sanusi Muhammad.

To sai kuma Alhaji Ibrahim Matawallen dan takarar gwamna na jam'iyyar adawa ta Labour ya ce gwamnatin jihar Bauchin na nade tabarmar kunya da hauka ne.

Shi ma Malam Nasiru Ibrahim Darazo, mataim akin a musamman ga dantakarar gwamna na jam'iyyar adawa ta ANC, Sanata Baba Tela, cewa ya yi gwamnatin jihar Bauchi ta Malam Isa Yuguda da kuma jam'iyyar PDP, suke haddasa tashin hankali.

Da na tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchin, ASP Muhammad Barau, kan lamarin ya ce bai da wata masaniya a kai don haka ba zai yi wani karin bayani ba.

Jihar ta Bauchi dai ta yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula na kabilanci da addini da kuma siyasa inda ko a jiya wasu bayanai sun ce mutum guda ya rasa ransa a wani lamari mai nasaba da sara-suka a cikin garin Bauchi.