Dr Goodluck na goyon bayan Farfesa Jega

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya nuna goyon bayansa ga shugaban hukumar zaben kasar, Parfesa Attahiru Jega, bayan matsalar da aka samu ta dage zabe.

A hirar da ya yi da sashen Turanci na BBC, shugaban Jonathan ya yi magana a karon farko a kan cece kucen da ya biyo bayan dage zaben majalisar dokokin tarayyar kasar, wanda aka shirya yi ranar asabar din da ta gabata.

Ya ce duk da yake bai ji dadin abin da ya faru ba, amma yana da kwarin gwiwar cewa Parfesa Jega zai iya sauke nauyin dake kansa na shirya zabe ingantacce a kasar.

Shugaba Jonathan ya bukaci jama'a su ci gaba da nuna hakuri da juriya, su kumafito domin yin zaben ranar Asabar mai zuwa.