Ana tattauna yadda Gbagbo zai bar mulki

Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tattauna yuwuwar sarandar Laurent Gbagbo

An shafe sa'o'i ana tattaunawa a garin Abidjan na kasar Ivory Coast game da sarandar Laurent Gbagbo, wanda ya ki amincewa ya sauka daga mulki, tun bayan da ya fadi zabe a watan Nuwamban bara.

Rahotanni sun ce fadan da ya barke a Abidjan tsawon kwanaki yanzu ya lafa.

Dakarun da ke goyon bayan mutumin da majalisar dinkin duniya ta amince da shi a matsayin shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara sun kewaye fadar shugaban kasar, in da rahotanni ke cewa Mr Gbagbo ya boye a cikin wata mafaka ta karkashin kasa.

Jami'an majalisar dinkin duniya sun ce ya amince da yin saranda sai dai ya na neman kariyar majalisar ya yinda kwamandojin da ke goyon bayan Mr. Outtara ke cewa sai dai ya mika wuya ba tare da wani sharadi ba.