Yawan aiki na iya haifar da ciwon zuciya

Yawan aiki na iya haifar da ciwon zuciya
Image caption Jama'a da dama na yin aiki fiye da sa'o'in da aka kayyade musu

Masana kimiyya sun ce yin aiki tsawon sa'o'i 11 maimakon 7 ko 8 da aka saba na kara yiwuwar kamuwa da ciwon zuciya.

Hadarin ya kai kashi 67 cikin dari kan mutanen da ke aiki na tsawon lokaci, a binciken da masana su ka wallafa a mujallar Annals of Internal Medicine.

Masanan na jami'ar University College London sun gudanar da binciken ne kan ma'aikata 7,000 wadanda aka bi diddigin lafiyarsu tun shekarar 1985.

Suka ce ya kamata likitoci su dinga tambayar marasa lafiya kan sa'o'in da su ke aiki.

Mutumin da ya jagoranci binciken Farfesa Mika Kivimäki ya ce: "La'akari da sa'o'in da jama'a ke aiki da kuma tattaunawa da su na da mahimmanci. Bincikenmu ya tabbatar da bukatar baiwa hakan mahimmanci.

"Binciken ya sa dole mu sauya tunanin da muke da shi na cewa 'wuya ba ta kisa' a cewar Farfesa Stephen Holgate na kungiyar Medical Research Council.

"Ya kuma kara nuna mana cewa ba wai kawai motsa jiki da sauya abubuwan da muke ci ne matsalolin da ya kamata mu lura da su ba".

"Zai kuma iya zamowa wata guduma ce ga jama'ar da suke aiki fiye da kima, musamman idan suna da wasu matsalolin na daban".

Akwai babbar damuwa

A shekaru 11 da aka shafe ana gudanar da binciken, mutane 192 da suka shiga cikin binciken sun kamu da cutar bugun zuciya.

Mutanen da ke aiki na tsawon sa'o'i 11 ko fiye da haka a rana, na cikin hadarin kamuwa da bugun zuciya fiye da wadanda ke aiki kasa da haka.

Kuma kara tsawon lokacin da jama'ar da ke fama da wasu cututtuka masu alaka da zuciya, kamar hawan jini, ya kara karfafa binciken da masanan suka yi.

Farfesa Peter Weissberg na gidauniyar British Heart Foundation ya ce: "Wannan binciken ya kara hasashen da ake da shi na cewa aiki na tsawon lokuta na iya kara hadarin kamuwa da cutar bugun zuciya.

"Amma akwai bukatar karin bincike domin tabbatar da hanyoyin da ya kamata a bi wajen tantance mutumin da ke dauke da cutar da kuma shawarar da ya kamata a bayar kan tsawon lokacin aiki".

Masana na ganin akwai dalilai da dama ciki har da hauhawar jini da gajiya da kuma yawan buri da ke iya taimakawa wajen yaduwar wannan matsalar.