An soma samun sakamakon zaben kasar Haiti

Mista Michel Martelly Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An fara bayyana sakamakon farko na zaben shugabankasar Haiti inda sakamakon ke nuna cewar mawaki Michel Martelly ne ke kan gaba

Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Haiti zagaye na biyu, na nuna cewa mawakin nan wato Michel Martelly, shine ke kan gaba.

Adadin kuri'un na nuna cewa Mista Martelly ya samu fiye da kashi biyu bisa ukku, inda ya doke matar tsohon shugaban kasar Mirlande Manigat.

Idan aka tabbatar da sakamakon zaben, Mista Martelly zai gaji shugaba Rene Preval, wanda yayi mulkin kasar na tsawon shekaru biyar.

Sabon shugaban kasar dai zai fuskanci kalubalen tunkarar annobar kwalera da kuma abubuwan da suka biyo bayan mummunar girgizar kasar da ta aukawa kasar a bara.