Ana cigaba da kokarin zakulo Laurent Gbagbo

Dakarun Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Alassane Ouattara

A Cote d'Ivoire, Lauren Gbagbo, wanda aka yi wa kawanya, ya ci gaba da boyewa a cikin gidansa a Abidjan, yayin da magoya bayan abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara, ke ta kokarin zakulo shi.

A lokacin da ya kira Gidan Rediyon Faransa ta wayar tarho tun farko a yau, Mr Gbagbo ya musanta rahotannin cewar yana cikin abinda ya kira gidan karkashin kasa.

Sabon fada ya barke da safiyar yau ne bayan rugujewar tattaunawar da ake yi don neman ya ba da kai.

Magoya bayan Mr Gbagbo sun ce masu hamayya da shi suna son kashe shi ne.

Sai dai jami'an Alassane Ouattara sun ce an baiwa dakarunsu umurnin su kama shi da ransa.