kwastan sun kama yunifom na soja a Kano

Wasu jami'an tsaro a Najeriya
Image caption Wasu jami'an tsaro a Najeriya

Hukumar kwastan ta Najeriya reshen jihar Kano, ta kama wasu yunifom na soja da aka yi kokarin shiga da su kasar ba tare da izni ba, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a Kanon.

Hukumar ta ce yunifom din na kunshe ne a cikin katun- katun takwas, kuma kowane katun yana dauke da yunifom ashirin zuwa ashirin da biyu.

Yanzu haka dai hukumar ta ce ta kama mutane biyu da ta mika wa jami'an tsaro.

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayanin inda aka nufin dosa da wadannan kayayyaki ko kuma abun da ake nufin yi da su.

Hukumar Kwatam din dai ta ce tana ci gaba da bincike a kan lamarin.