Laurent Gbagbo yaki ya mika kai

Shugaba Gbagbo na Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabankasar Ivory Coast Laurent Gbagbo yaki amincewa ya sauka daga kan kujerar mulkin kasar duk kuwa da kawanyar da sojoji sukai wa gidan da yake ciki

Shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo wanda yake buya a karkashin fadarsa ta shugaban kasa, ya ki sauka daga kan karagar mulki duk kuwa da kawanyar da dakarun dake biyayya ga abokin hamayyarsa Alassane Ouattara suka yi masa.

Mista Gbagbo ya shaidawa gidan talabijin na kasar Faransa cewa ya amince da tattaunawa tare da Mista Ouattara, kuma ya yarda a sake kidaya kuri'un zabenda aka gudanar a watan Nuwambar bara, amma yace ba zai mika wuya ba.

Wakilin BBC ya ce watakila abinda Mista Gbagbo ke so shine wata kasar da za ta karbe shi.

To sai dai a baya bangaren Mista Ouatarra sun yi kira da a gurfanar da Laurent Gbagbo a gaban kuliya, saboda laifukan yaki da suke zarginsa da aikatawa.