Hujjar cigaba da tsare Mamadou Tandja

Mamadou Tandja
Image caption Mamadou Tandja

A jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun yi karin haske a game da shari'ar tsohon shugaban kasar Malam Mmamadou Tandja.

A jiya ne kotun daukaka karar kasar ta yi ma tsohon shugaban kasar sakin talala, amma gabanin a sallami shi daga gidan kurkukun KOLLO, sai gwamnatin Niger din ta shigar da wata sabuwar kara a kan shi.

Sai dai a wata hira da BBC ministan shari'ar kasar, Abdoulaye Djibo ya ce yanzu ana zargin Malam Mamadou Tandja ne da hannu a cikin salwantar da wasu kudade a kamfanin samar da takin zamani na kasa, da kuma kin bin umarnin kotun tsarin mulki a kan haramcin da ta yi ma shirin Tazarce a 2009.

Sai dai lauyan tsohon shugaban kasar,Barista Souley Oumarou ya ce wata bita da kullin siyasa ce ake yi ma Malam Mamadou Tandja.