Jam'iyyun adawa na fargabar sake dage zabe

Farfesa Attahiru Jega, Shugaban hukumar zaben Najeriya
Image caption Wasu jam'iyyun adawa a Najeriya sunce sam ba zasu amince da duk wani shiri na fasa yin zabukan 'yan majalisu a wasu bangarorin kasar ba a ranar asabar mai zuwa.

A Najeriya yayin da ake hasashen cewa maiyiwuwa za a fasa gudanar da zaben 'yan majalisun dokokin kasar da aka shirya gudanarwa ranar asabar mai zuwa a wasu jihohin kasar saboda wasu matsalolin da suka shafi karanci da rashin daidaiton kayan zabe, jam'iyyar adawa ta ACN ta ce ba ta yarda da wannan shirin ba

Jam'iyyar ta bayyana cewar wannan wani take-take ne na bude kafar yin magudi da bangar siyasa.

Maimakon haka, a cewar jam'iyyar, kamata ya yi hukumar zaben kasar ta gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi, idan ta samu cikakken kayan zabe sai ta gunanar da zaben 'yan majalisun dokokin tarayya.

Sai dai hukumar zaben kasar wato INEC ta ce kawo i yanzu ita ba ta yanke hukunci akan ko za ta fasa gudanar da zaben 'yan majalisun tarayyar ba a wani bangare na kasar