Bahrain ta musanta zargkin cin zarafin BilAdama

Masu zanga-zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto re
Image caption Masu zanga-zanga a Bahrain

Bahrain ta ce babu wata tartibiyar shaidar da za ta goyi bayan zargin da kungiyoyin kare hakkin Bil adama suka yi na cewar ta zafafa wani kamfe na cin zarafin wadanda suke zargin suna da hannu a cikin zanga- zangar kin jinin gwamnati.

Hukumomin Bahrain din musamman sun yi magana game da zargin da Kungiyar bayar da taimakon likitoci ta MSF ta yi na cewar dakarun tsaro suna kama majinyata su kuma lankada ma su duka a cikin babban asubitin Bahrain.

Suka ce masu zanga- zanga sun kwace asibitin , abinda ya kawo cikas gaya ga ayyukansa, kuma matakin da yansanda suka dauka na karbe ginin abu ne da ba yadda za a kauce masa.