An kara dage zabe a wasu sassan Najeriya

Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfes Attahiru Jega

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce ba za'a yi zaben 'yan majalisu a wasu sassan kasar ba a ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega ya ce za'a yi zabukan da aka dage ne a ranar 26 ga watan Afrilu.

Ba za a yi zabe a mazabun majalisar dattawa goma 15 ba da kuma na 'yan majalisar wakilai 48.

Najeriya dai na da kujerun 'yan majalisar dattijai 109 ne da kuma na majalisar wakilai 360.

Farfesa Jega ya ce an dage zaben ne a wadannan yankunan saboda ko dai an riga an yi amfani da takardun kada kuria na wadannan yankunan a ranar Asabar din da ta gabata, ko kuma babu alamar wasu jam'iyyu a kan takardun kada kuri'ar.

Dagewar a yanzu za ta baiwa hukumar damar buga wasu sabbin takardun kada kuri'ar, kuma a yanzu za a gudanar da zaben ne a wadannan yankunan a ranar 26 ga watan Aprilu tare da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi.

A ranar 2 ga watan Afrilu ne dai aka shirya zaben 'yan majalisa a Najeriya, amma hukumar ta dage saboda rashin isassun kayan aiki.

Tun da farko hukumar zaben ta dage zaben ne zuwa ranar 4 ga watan Afrilu sannan kuma ta kara dagewa zuwa ranar 9 ga watan Afrilu.

Mazabun 'Yan Majalisar Dattijai da na Wakilai da aka dage zabensu daga ranar 9 ga watan Aprilu zuwa 26 ga watan Aprilu 2011
S/N Jiha
Majalisar Dattijai Majalisar Wakilai
1 ABIA 1 Isialangwa North/South
2 AKWAIBOM 2 Ukanafu/Orun
3 ANAMBRA 3 Anambra East & West
4 4 Nnewi/Ekwusigo
5 5 Oyi/Anyamelu
6 BAYELSA 1 Bayelsa Central
7 BENUE 2 Benue North
8 6 Gwer East/West
9 7 Katsina Ala/Ukum
10 CROSS RIVER 3 Southern District
11 4 Central District
12 8 Abi/Yakurr
13 DELTA 9 Aniocha/Oshimili
14 10 Ethiope East/West
15 11 Bomadi/Patani
16 EBONYI 5 Ebonyi North
17 12 Ohaozara/Onichal/Ivo
18 EDO 13 Akoko Edo
19 EKITI 6 Ekiti Central
20 7 Ekiti North
21 8 Ekiti South
22 14 Ado Ekiti/Irepodun/Ifelodun
23 15 Ido/Osi/Moba/Ilejemeje
24 16 Ijero/Ekiti West/Efon
25 17 Ikole/Oye
26 GOMBE 9 Gombe North
27 18 Yamaltu/Deba
28 19 Kaltungo/Shongom
29 20 Dukku/Nafada
30 IMO 21 Okigwe/Iheme/Mbanu
31 JIGAWA 22 Taura/Ringim
32 KADUNA 10 Kaduna North
33 23 Ikara/Kubau
34 24 Kachia/Kagarko
35 25 Kauru
36 26 Makarfi/Kudan
37 KADUNA 27 Z/Kataf/Soba
38 KANO 28 Dala
39 29 Gwarzo/Kabo
40 30 Karaye/Rogo
41 KWARA 31 Ekiti/Oke Ero/Isin/Irepodun
42 LAGOS 32 Ifako/Ijaye
43 33 Shomolu
44 34 Ikorodu
45 NASARAWA 35 Keffi/Kokona/Karu
46 NIGER 11 Niger South
47 36 Bida/Gbako/Katcha
48 37 Lavun/Edasi/Mokwa
49 OGUN 38 AbeokutaObafemi-OwodeOdeda North/ 1
50 39 Ijebu Ode/Odogbolu/Ijebu North-East
51 40 Egbado South/Ipokia
52 OGUN 41 Ijebu North/IjeguOgun North East/ Water Side
53 42 Ikenne/Shagamu/Remo North
54 OYO 43 Ibadan NW/SW
55 PLATEAU 12 Plateau North
56 13 Plateau Central
57 14 Plateau South
58 44 Jos North/Bassa
59 45 Pankshin/Kanke/Kanam
60 RIVERS 46 Port Harcourt 2
61 SOKOTO 15 Sokoto North
62 ZAMFARA 47 Anka/T. Mafara
63 48 Zurmi/Shinkafi