An rantsar da sabon shugaban kasar Nijar

Image caption Sabon Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou

A yau ne aka rantsar da Shugaba Issoufou Mahamadou a matsayin shugaban kasar Nijar.

Shugabar Majalisar tsarin mulki ta kasar ce Fatimata Bazeye ce ta gabartar da ranstuwar da sabon shugaban ya sha na kama aiki.

An dai gudanar da taron ne a filin wasa na Senyi Kountche da ke babban birnin kasar, Niamey.

Rantsarwar ta sa ta kawo karshen mulkin wucin gadinda majalisar mulkin sojin kasar wadda ta hambarar da gwamnatin Tandja Mamadou a watan Fabrairun bara ta yi, biyo bayan yunkurin tazarcen da yayi.

Shugaba Mahamadou Issoufou da yake rantsewa da Al'qur'ani mai girma ya ce:

"Na yi rantsuwa ga Allah zan kare kundin tsarin mulkin Nijar, kuma zan kare martabar kasarmu, kuma in tabbatar da adalci da kuma inganta rayuwar al'ummarmu."

Sabon shugaban kasar ya karrama shugaban mulki soji mai barin gado, wato Janar Salou Djibo da babbar lamabar yabo ta kasa ta GCN.

Tuni dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta CSRD da wasu muhimman ma'aikatu da ta kafa domin taya ta aiki a karkashin gwamnatin wucin gadin kamar Majalisar Tuntubar juna ta CCN, suka soma mika sakamakon ayyukanda suka gudanar.

Manyan shugabannin Afrika da su ka hada na kasashen Congo da Senegal da Togo da Liberia da Mali da Benin da kuma Gabon ne suka halarci taron rantsarwar.

Har wa yau kasashen Najeriya da Ghana da Aljeriya da Gambia da Faransa da Chadi da Equatorial Guinea sun turo wakilansu a taron.