Bikin rantsar da sabon shugabankasar Nijar

Malam Mahammadou Issoufu
Image caption Sabon shugaban kasar Nijar Mahammadou Issoufu

A jamhuriyar Nijar idan an jima a yau ne ake sa ran za a rantsar da sabon shugaban kasar, wanda aka zaba a watan jiya, wato Injiniya Mahammadou Issoufu.

Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu ne a zaben shugaban kasar da ya aka yi zagaye na biyu.

Rantsarwar ta sa za ta kawo karshen mulkin wucin gadin majalisar mulkin sojin kasar wadda ta hambarar da gwamnatin Tandja Mamadou a watan Fabrairun bara biyo bayan yunkurin tazarcen da ya yi.

Tuni dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta CSRD da wasu muhimman ma'aikatu da ta kafa domin taya ta aiki a karkashin gwamnatin wucin gadin kamar Majalisar Tuntubar juna ta CCN, suka soma mika sakamakon ayyukanda suka gudanar.