Burtaniya na neman inganta kai agaji Libya

Andrew Mitchell
Image caption Sakataren Raya Kasashe Andrew Mitchell

Sakataren Raya Kasashe na Burtaniya, Andrew Mitchell, zai je birnin New York yau Litinin don tattaunawa da jami'an Majalisar Dinkin Duniya dangane da halin ha'ula'in da al'ummar Libya ke ciki.

Ana dai kara nuna damuwa ne dangane da halin da fararen hula—wadanda fada ya rutsa da su a Misrata da sauran sassan kasar Libya—ke ciki.

Hukumar Raya Kasashe ta Burtaniya ta bayyana yanayin da cewa ya yi muni.

A cewar Hukumar, ana kyautata zaton an kashe fararen hula akalla dari uku, an kuma raunata wasu dubu daya a Misrata kadai.

Makasudin ziyarar da Mista Mitchell zai kai Majalisar ta Dinkin Duniya dai shi ne gano hanyoyin da ya kamata a bi don kara yawan kayan agajin da ake kaiwa yankin.

Tuni dai jiragen ruwa da dama, ciki har da wadanda Burtaniya ta dauki nauyinsu, suka samu damar kai kayan agaji sannan kuma suka kwashe wadansu mutane daga garin na Misrata.

Sai dai ranar Juma'a Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa aikin agajin na fuskantar karancin kudade sannan kuma akwai dubban mutanen da ya kamata a kwashe a kasa.