Sojin Masar sun tarwatsa masu zanga-zanga

Masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir

Sojojin Masar sun tarwatsa masu zanga-zangar da suka ci gaba da kasancewa a Dandalin Tahrir bayan zanga-zangar da aka yi jiya Juma'a domin neman a hukunta tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak, da wadansu na kusa da shi.

Sojojin dai sun aukawa Dandalin na Tahrir ne da sanyin safiyar yau Asabar, inda suka yi ta harbi a sama, kana suka yi amfani da kulake wajen korar masu zanga-zangar.

Dandalin Tahrir dai ya kasance matattarar zanga-zangar da ta kai ga kawo karshen mulkin Hosni Mubarak a watan Fabrairun da ya gabata.

Masu zanga-zangar dai sun ce ba su gamsu da yadda hukumomin sojin kasar—wadanda suka karbi mulki daga Mista Mubarak—suka gaza kawo sauye-sauyen siyasa a kasar ba.