Mutanen Iceland sun juyawa gwamnati baya

Bankin Iceland wanda ya durkushe Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bankin Iceland wanda ya durkushe

Wani bangare na sakamakon zaben raba-gardamar da aka gudanar a Iceland ya nuna cewa ga alamu al'ummar kasar sun ki amincewa kasar ta biya gwamnatocin Burtaniya da Holland dala biliyan biyar.

Wannan zabi na al'ummar Iceland dai ka iya yin kafar ungulu ga yunkurin da kasar ta ke yi na shiga kungiyar Tarayyar Turai.

Ana dai kallon wannan zaben raba-gardamar a matsayin wani muhimmin matakin sake gina kasar ta Iceland, wadda koma-bayan tattalin arzikin da duniya ta fuskanta a 2008 ya yi wa kacakaca.

Bankunan kasar guda uku ne dai dimbin bashi ya sa suka durkushe.

Daya daga cikinsu kuma shi ne Landsbankinn, wanda ya yi asarar dala biliyan biyar—ajiyar 'yan Burtaniya da 'yan Holland, wadanda gwamnatocin kasashensu suka biya su diyya.

Gwamnatin kasar ta Iceland ta yi alkawarin mayar wa gwamnatocin kasashen biyu kudadensu tana mai fatan za ta samu shiga kungiyar Tarayyar Turai.

Sai dai 'yan kasar ta Iceland da dama sun fusata da yadda kasar ta su ke neman daukar asarar da suke ganin hadamar wadansu ma’aikatan bankuna ce ta haifar da ita.

Don haka ne suka yi fatali da wannan bukata a karo na biyu.