Jam'iyyar Kwaminis za ta sha kaye a Indiya

Masu zabe a Jihar Yammacin Bengal Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zabe a Jihar Yammacin Bengal

Bisa ga dukkan alamu gwamnatin Jam'iyyar Kwaminis mafi dadewa a duniya—wadda kuma zabar ta aka yi—na fuskantar shan kaye a siyasance, yayin da aka soma kada kuri'ar zaben sabuwar majalisar dokoki a Jihar Yammacin Bengal ta Indiya.

Jam'iyyar ta Kwaminisanci, wadda take lashe zabe tun daga shekarar 1977 a jihar ta Yammacin Bengal, na fuskantar kalubale ne mafi girma daga ’yan adawa a karkashin jagorancin Ministar Zirga-zirgar Jiragen Kasa ta Indiya, Mamata Banerjee.

Ministar dai ta zargi Jam'iyyar Kwaminisancin da gaza cimma bukatun al'ummar Jihar su miliyan casa'in.

Wannan al’amari, in ji Ministar, ya jefa Jihar cikin tsaka mai wuya ta fuskar tattalin arziki.