An kwashe jami'an Burtaniya daga Abidjan

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

An kwashe mutanen da ke ofishin jakadancin Burtaniya a Ivory Coast sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun da ke biyayya ga mutanen da ke takaddama a kan shugabancin kasar ta Ivory Coast.

Ofishin jakadancin na Burtaniya dai ba shi da nisa daga gidan Shugaba Laurent Gbagbo, wanda ya kekasa kasa ya ki mika mulki duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya da ma akasarin kasashen Afirka sun yi amannar cewa shi ne ya sha kaye a zaben watan Nuwamban bara.

Gidan na Mista Gbagbo dai ya fuskanci hare-hare daga dakaru masu biyayya ga Alassane Ouattara, wanda kasashen duniya suka ce shi ne ya lashe zaben.

Kwanan baya dai dakarun da ke biyayya ga Mista Ouattara sun yi nasarar kwace sassa da dama na kasar, amma kuma yanzu suna fuskantar matsananciyar turjiya a yunkurinsu na kwace birnin Abidjan.

Daya daga cikin ma'aikatan ofishin jakadancin na Burtaniya ya ce sun yanke shawarar barin wurin ne bayan harsashi ya fara shiga ta taga yayin da bama-bamai suka fara dira a farfajiyar ofishin.

Jiya Asabar ne dai wani ayarin motoci masu sulke na Majalisar Dinkin Duniya suka kwashe jami'an diflomasiyyar Burtaniya biyu da kuma ma'aikata goma sha shida 'yan asalin kasar ta Ivory Coast.

Akalla mutane miliyan daya ne dai—wadanda ke fuskantar karancin abinci da ruwan sha—fadan ya raba da gidajensu.