'Libya na amfani da haramtattun makamai'

Daya daga cikin bama-baman da aka haramta Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Daya daga cikin bama-baman da aka haramta

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Libya da amfani da samfurin makaman da aka haramta amfani da su a fadin kasashe dari na duniya.

Sai dai gwamnatin ta Libya ta musanta zargin.

Human Rights Watch ta ce daya daga cikin masu daukar mata hoto ya ga akalla uku daga cikin irin bama-baman na fashewa a wani yanki na gidajen jama'a a a Misrata inda magoya bayan Gaddafin suka tsananta kai hari.

Ta kuma ce alamu sun nuna cewa a Spain aka kera bama-baman sai dai babu wani martani da gwamnatin Spain din ta mayar a kan wannan ikirari.

Karin bayani