Zaben 'yan majalisar tarayya a Najeriya

Zaben 'yan majalisar tarayya a Najeriya
Image caption Sau uku dai ana dage zaben 'yan majalisun

A Najeriya, a ranar Asabar ne ake sa-ran gudanar da zaben `yan majalisun dokokin kasar, kuma shi ne zai share hanya ga zabukan shugaban kasa da na gwamnoni da ke biye.

`Yan majalisu na da muhimmanci a tsarin mulkin demokuradiyya, saboda su ne da alhakin tsara dokokin kasa.

To sai dai wasu `yan Najeriyar na sukar rawar da `yan majalisun ke takawa, bisa zargin cewa mafi yawansu `yan amshin shata ne, amma suna musantawa.

Kasancewar `yan majalisun dokoki da suka hada da `yan majalisar dattawa da na wakilai da kuma majalisun jihohi wani bangare ne a tsarin mulkin demokuradiyya da su aka yi ta damawa a mulkin Najeriya tun da kasar ta sake komawa ga turbar demokuradiyya sama da shekaru goma sha biyu da suka wuce.

Kuma a tsawon wannan lokacin wannan ne karo na hudu da za a gudanar da zabe na bai-daya na `yan majalisar dattawan da `yan majalisar wakilai ta kasa.

Kuma `yan takara daga jam`iyyun siyasar kasar sama da sittin ne za su jarraba sa`a a kan kujeru dari da tara da ke majalisar dattawa, yayin da majalisar wakilai ta kunshi kujeru dari uku da sittin.

Cancanta ko rashinta

Ko da `yan majalisun dokokin Najeriyar da aka dama da su a wannan tsakanin na ikirarin zartar dokoki daban-daban da suke cewa sun shafi rayuwar jama`a tare da sa-ido a kan ma`aikutun gwamnati don tabbatar da cewa ayyuka na tafiya yadda ya kamata.

Haka kuma `yan majalisun tarayyar na buga-kirji da cewa bisa jajircewarsu ce akidar ta-zarce ta wargaje a shekara ta 2006.

Kazalika a cewarsu, rawar da suka taka a lokacin rasuwar shugaba Umaru Musa `Yar'adua ce ta taimaka wajen daidaita lamura a kasar.

Sai dai mafi yawan `yan Najeriyar na sukar `yan majalisar da cewar ba su tabuka wani abin kirki ba.

Har ta kai ga wasu `yan kasar na yi musu lakabi da sunaye iri-iri suka hada da `yan amshin-shata ko dumama kujera, saboda zargin da wasu ke yi cewar bayan zabe, wasu `yan majalisar ba a jin duriyarsu.

`Yan Najeriyar dai suna da babban kalubale a gabansu na danne kwadayi da son zuciya wajen zabar `yan takarar bisa cancanta, saboda `yan magana sun ce kowa ya bi son zuciya to zai ga bacin zuciya.