Ba za mu nemi afuwa ba - In ji Nato

Ba za mu nemi afuwa ba - In ji Nato Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mataimakin kwamandan Nato ya ce ba za su naimi afuwa ba

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce ba za ta nemi gafara bisa harin da ta kai da jiragen sama kan kuskure a kan tankokin yakin yan tawaye a kusa da Ajdabiya a Gabashin Libya.

Lamarin dai ya haifar da asarar rayuka da dama.

Mataimakin Kwamandan aikace-aikacen kungiyar ya shaida wa wani taron manema labarai cewar yanayi a lokacin ya kasance marar tabbas, inda tankoki ke zirga-zirga ta bangarori daban daban.

Ya kara da cewa kungiyar ta NATO ba ta da masaniyar cewar 'yan tawayen na amfani da tankokin yaki.

Tun farko dai Kwamandan dakarun 'yan adawar ya ce kungiyar ta NATO ta nemi afuwa.

Ya kuma yi watsi da batun cewa akwai bukatar Nato ta inganta sadarwa tsakaninsu da 'yan tawayen, yana mai cewa wannan ba aikinsu ba ne.

Tun da fari dai a wata sanarwa da kwamandan 'yan tawayen janar Yunus ya bayar, ya ce an gargadi Nato da cewa an kai tankunan yaki bakin daga.

Wani mai magana da yawun 'yan tawayen kanal Ahmed Omah Bani ya shaida wa BBC cewa ya gamsu da martanin da kungiyar ta NATO tayi game da al'amarin.

Yace: "A halin da ake ciki, ni a nawa ra'ayin duka daya ne, idan sun nemi gafara za mu ji dadin hakan, idan kuma basu nema ba suna da nasu dalilan na kin yin hakan, don haka ni na gamsu".