Wani abu ya fashe a Ofishin Hukumar zabe a Suleja

 Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega, Shugaban Hukumar zabe a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu wasu da yawa kuma suka ji raunuka a sanadiyar fashewar wani abu a Ofishin hukumar zabe dake Suleja a Jihar Neja, yayinda 'yan bindiga suka harbe wasu mutanen a Borno.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ma'aikatan zabe ke karbar kayan aiki.

Wani wanda ya shaida lamarin da ya auku a Suleja ya ce mafi yawan wadanda hadarin ya rutsa da su 'yan bautar kasa ne da aka dauka domin yin aikin zabe.

Hukumar zaben Najeriya da kuma Rundunar 'yan sandan Jihar Neja sun tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ba su bada adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.

Mai magana da yawun hukumar SSS ta kasa ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, akalla mutane shida ne suka mutu, amma kuma har yanzu suna ci gaba da samun bayanai ne kan batun.

Mahukuntan Najeriyar dai na zargin cewa abin da ya fashe din bom ne.

Shi ma shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce tuni ya bayar da umarnin kara tsaurara matakan tsaro a ofisoshin hukumar zabe da ke duk fadin kasar.

Shugaban ya yi Allahwadai da abinda ya faru a Sulejan.

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda da ke garin Shani na jihar Borno a daidai lokacin da ake rabon kayan aikin zabe.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a harin.

Ana dai ta'alaka harin da hare-haren da 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul Sunnah lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram.

'Yan bindigar dai sun kai harin ne kan ofishin 'yan sandan a dai-dai lokacin da ake kai musu kayayyakin zabe domin ajiyewa kafin zaben da za a gudanar gobe.

Hare-haren na faruwa ne kwana daya kafin soma babban zaben kasar wanda aka dage a karshen makon da ya gabata saboda rashin wasu kayan aiki.