Ana ci gaba da samun sakamako a Najeriya

Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Yau Litinin ne ake sa ran samun karin sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin Najeriya wanda aka yi ranar Asabar din da ta gabata.

Alamu dai na nuna yiwuwar raguwar yawan kujerun da jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ke rike da su, amma duk da haka akwai yiwuwar jam'iyyar za ta ci gaba da kasancewa mai rinjaye a majalisar.

Yayin da ake ci gaba da fitar da sakamakon zaben dai jam'iyyun adawa na CPC da kuma ACN sun samu nasara sosai.

Sai dai a wasu jihohin da suka sha kaye, ‘yan jam’iyyar CPC sun ce za su kalubalanci sakamakon.

Tuni dai jam’iyyar a jihar Sokoto—inda jam’iyyar PDP ta lashe kujeru biyu na ‘yan Majalisar Dattawa da kuma daukacin kujerun Majalisar Wakilai—ta yi watsi da sakamakon.

Jam’iyyar ta CPC da tana zargin an aikata laifuffukan zabe ne wadanda suka hada da tursasa wa masu zabe, da amfani da kudi, da kuma karkata akwatunan zabe a wadansu wurare.

A jihar Zamfara kuwa, inda wakilin jam’iyyar PDP ne a wurin tattara sakamakon zaben dan Majalisar Dattawa na Zamfara ta Tsakiya ya ki rattaba hannu a kan takardar sakamakon.

A cewarsa ya yi hakan ne saboda wakilansa a kananan hukumomi ukun da ke yankin ba su bi sakamakon ba kuma ba su kai masa kwafe na sakamakon zaben a yankunansu ba.

Jam’iyyar adawa ta ANPP ce dai ta lashe kujerun Majalisar Dattawa biyu a Jihar, PDP mai mulki kuma ta lashe daya; ANPP din ce kuma ta lashe uku daga cikin mazabun ‘yan Majalisar Wakilai hudun da aka yi zabe.

A Gombe kuma, jam’iyyar CPC ce ta ce za ta kalubalanci zaben Gwamna mai ci Alhaji Muhammadu Danjuma Goje a matsayin dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Gombe ta Tsakiya.

Hukumar zabe dai ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ta lashe kujeru biyu na zabukan Majalisar Dattawan da aka yi a jihar, na Gombe ta Tsakiya da kuma Gombe ta Kudu, inda tshohon mataimakin gwamnan jihar Barista Joshua Lidani ya lashe.

Ba a dai yi zaben a mazabar dan majalisar dattawa ta arewacin Gombe ba.

A zaben Majalisar Wakilai kuwa, a cewar shugaban hukumar zaben jihar, Godfrey Miri, jam’iyyar CPC ta ci mazabar Gombe Kwami Funakaye yayin da jam’iyyar PDP mai mulki ta ci mazabun Akko da kuma Billiri da Balanga.

Dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar CPC, Alhaji Abubakar Aliyu, ya yi zargin cewa an yi magudi musamman a mazabar dan Majalisar Dattawa ta Gombe ta Tsakiya.

Sai dai shugaban hukumar zabe a jihar ta Gombe ya yi watsi da zargin yana mai cewa hukumar ta yi zabe na adalci.

A jihar Borno kuwa rahotanni sun nuna cewa Gwamna mai ci, Ali Modu Sharif ya sha kaye a zaben dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Tsakiya.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa jam'iyyar PDP ce ke da galaba a mazabun Borno ta Tsakiya da ta Kudu, yayin da Jam'iyar ANPP mai mulkin jihar ta samu kujerar Arewacin Borno.

A jihar Yobe kuma, jam'iyyar ANPP, wadda ta kwashe shekaru 12 tana mulkin jihar, ta lashe kusan dukkannin kujerun Majalisar Dokokin.

Rahotanni daga Jihar Katsina kuma sun nuna cewa Jam'iyyar CPC ce ta lashe akasarin kujerun da aka fafata a kansu.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar zaben a Katsina, Malam Muhammad Musa Sokoto, ya shaidawa wakilin BBC cewa jam'iyyar ta CPC ce ta lashe dukkan kujeru uku na Majalisar Dattawa da kuma kujeru goma sha-biyu na Majalisar Wakilai; jam'iyyar PDP kuma ta yi nasarar samun biyu, yayin da kujera daya ta Dutsin-Ma da Kurfi sai nan gaba za a yi zaben saboda mutuwar dan takarar jam'iyyar ACN.

A cikin mutanen da suka rasa kujerun su a jihar ta Katsina har da gagarabadau na Majalisar Dattawa, Sanata Mahmoud Kanti Bello, da Sanata Ibrahim Ida, Shugaban kwamitin tsaro a Majalisar Dattawan.

Ita ma Hajiya Maryam Umaru 'Yar'aduwa, diyar marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa, wadda ta shiga takarar kujerar Majalisar Wakilai a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaben.

Karin bayani