An bude sabuwar Majalisar dokokin Niger

A Jamhuriyar Niger, yau ne sabuwar majalisar dokokin kasar ta yi zamanta na farko tun bayan zaben yan majalisar dokokin da aka yi a watan janairun da ya gabata .

A zaman nata majalisar ta zabi shugabani na rikon kwarya tare da tsaida wani jadawali na kwanaki uku domin tsara dokokin tafiyar da ayyukanta.

Hakan dai zai bada damar zaben kakakin majalisar da komitoci na gudanarwa na dindindin.

Sai dai tuni wasu yan kasar suka soma isar da koken su ga wannan sabuwar majalisa