Syria za ta dauki mataki a kan masu fafutuka

Masu zanga-zanga a Homs Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Homs

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar Syria ta ce boren da ake yi a kasar tamkar tayar-da-kayar-baya ne da makamai.

Ma’aikatar ta kuma ce za ta dauki kwararan matakai domin tabbatar da tsaro da daidaita al'amura a kasar.

Wannan sanarwar dai ta zo ne bayan 'yan adawa sun mamaye tsakiyar birnin Homs, wanda shi ne na uku mafi girma a kasar.

Sai dai kuma masu fafutuka sun ce ba za su bar tsakiyar birnin ba har sai an biya musu bukatunsu na sauyi a siyasar kasar.

Bukatun dai sun hada ne da dage dokar ta-bacin da ke aiki a kasar ta Syria tsawon shekaru da dama.