Dakarun Laurent Gbagbo sun yi nasara

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Abidjan
Image caption Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Abidjan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce shugaban kasar Ivory Coast wanda ya ki mika mulki, Laurent Gbagbo, ya yi nasara a yakin da ake fafatawa don karbe iko da birnin Abidjan.

Babban jami'in kiyaye zaman lafiya na Majalisar, Alain Le Roy, ya ce dakarun Mista Gabgbo sun yi amfani da tsagaita wutar da aka yi ana tattaunawa don sake jan damara.

Mista Le Roy ya ce yanzu haka dakarun Laurent Gbagbo ne ke iko da unguwar da fadar shugaban kasar ta Ivory Coast ta ke.

A cewarsa har yanzu dakarun na Mista Gbagbo na dauke da manyan makamai duk da harin da dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na Faransa suka kaiwa ma'ajiya makamansu a farkon wannan makon.

Bayan harin ne ma dai manyan jami'an sojin Mista Gbagbo suka nemi a tattauna don kawo karshen yakin da suke fafatawa da dakarun Alassane Ouattara, wadanda suka yi wa Mista Gbagbo kawanya.

Sai dai, a cewar Mista Le Roy, ashe dabara ce kawai.

Mista Le Roy ya ce ga alamu dakarun na Mista Gbagbo sun dumfari hedkwatar Mista Ouattara wadda suke ta harba rokoki kusa da ita.

Karin bayani