An aikewa Hosni Mubarak sammaci

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomin kasar Masar sun gabatar da sammaci ga tsohon shugaban kasar , Hosni Mubarak, domin ya zo ya amsa tamboyi, kuma sun tsare tsohon firamininstansa, Ahmed Nazif a gidan yari, bisa zargin sama da fadi da wasu kudaden gwamnati.

Mr. Nazif dai shine wani babban jami'i a gwamnatin Mubarak da za'a tsare tun bayan lokacin da aka tilastawa sauka daga shugabancin kasar watanni biyu da suka wuce.

Masu shigar da kara kuma na son su yiwa 'ya'yan Mr Mubarak su biyu wato Alaa da Gamal wasu tambayoyi.

Sai dai a jawabin farkon da ya gabatar tun bayan da ya sauka daga kan mulki Mr Mubarak ya musanta zargin da ake yi masa na tara dukiya ta haramciyyar hanya a shekaru talatin da ya shafe yana mulki.

Ya kuma ce zai hada kai da hukumomin kasar domin wanke sunan iyalinsa daga duk wani zargi.