Isra'ila da Hamas na san sasatanwa

Isra'ila da kungiyar Palasdinawa ta Hamas wadda ke iko da Zirin Gaza, duk sun ce a shirye suke su kawo karshen hare haren da suke kaiwa juna, muddin daya bangaren ya dakatar da kai nasa hare haren.

Sai dai praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila zata maida martani mai zafi, idan aka ci gaba da harba rokoki daga Gaza.

Wakilin BBC ya ce wani mai magana da yawun Kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya ce muddin Israela ta daina muzguna musu, to tabbas za'a samu kwanciyar hankali. A 'yan kwanakin da suka wuce, rahotanni sun nuna cewa an harba rokoki sama da dari, zuwa kudancin Isra'ila.